Episódios
-
Tare da goyon bayan @pulitzercenter, wannan shirin na #BIRBISHINRIKICI ya duba labarin wata mata da ta auri wani dan kungiyar #BokoHaram Wanda yanzu aka ma gyaran hali, da kuma yadda abin da ya faru a baya ke shiga tsakani halin da suke ciki a yanzu a yankin da aka sake tsugunar da su a jihar Borno.
Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Marubuciya: Hauwa Shaffii Nuhu
Muryoyin Shiri: Khadija Gidado
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
A watan Disambar 2023, wasu da ake zargin mayakan Ambazoniya ne suka kai hari kan al'ummar Belegete a Cross River, Kudu-maso-Kuducin Najeriya, wani ƙauye mai iyaka kusa da Kamaru.
A cikin wannan shirin na #BirbishinRikici, za mu ba da labarin Elizabeth, mahaifiyar 'ya'ya shida, wacce ta tsere daga harin kuma ta sami mafaka a wani wurin kiwon dabbobi da ke kusa.
Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Muryoyin Shiri: Khadija Gidado
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
Estão a faltar episódios?
-
A cikin shirin #BirbishinRikici, za mu kawo muku labarin Aisha, wacce aka yi garkuwa da ita tana da shekaru sha takwas, aka yi mata auren dole da wani dan Boko Haram. Bayan shekaru takwas, ta tsere a matsayin mahaifiyar 'ya'ya hudu. Yanzu, tana bin burinta da kwato 'yancinta.
Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Muryoyin Shiri: Khadija Gidado
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
A shirin #BirbishinRikici na yau, muna ba da labarin Hauwa Abbagana, wata budurwar amarya da aka sace. Bayan tserewa daga zaman talala, ta dawo gida ciki da ɗan wanda ya zalunce ta, cikin fargabar kyama da ƙi da za ta iya fuskanta.
Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Muryoyin Shiri: Khadija Gidado, Samir Sheriff
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
Babu wanda ya ga hakan yana zuwa, yayin da mutanen kauyen suka shirya kansu domin murnar bukukuwan, ‘yan bindiga na kan hanyarsu ta zuwa yanka su. An kai wa kananan hukumomi uku hari a jihar Filato a Najeriya, inda aka kashe mutane kusan 195 da kuma abubuwan tunawa da mutane suka yi a kusa da gidajensu.
Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Muryoyin Shiri: Khadija Gidado, Hajara Ibrahim, Akila Jibrin Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
A shiri na yau, zamu ba da labarin Rukayya Saidu, wata uwa mai yara biyu da aka kona gidanta a Kaku, amma tana sake gina rayuwarta yanzu a Kajuru, Arewa maso Yammacin Najeriya.
Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
A yau za mu ji labarin Umar, wani Bafulatani da ya sha fama da hare-haren ta’addanci a kauyensu, sannan ya ga al’ummar da yake zaune a cikinsa sun juya masa baya ba gaira ba dalili sai asalinsa. Umar, kamar sauran jama’a, ya kasance wanda aka zalunta dan kabilanci. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Muryoyin Shiri: Akila JibrinFassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
A lokacin da ake fama da hare-haren Boko Haram a Najeriya, an samu asarar rayuka da dama. Binciken HumAngle ya gano cewa ana jibge gawarwaki da dama da ba a san ko su waye ba a asibitin kwararru na jihar Borno. Kusa da asibitin al’ummar Hausari ne, kuma suna da koke-kokensu.
Muryoyin Shiri: Akila Jibrin, Samir Sherrif, Aliyu Dahiru
Fassara: Rukayya SaeedEdita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
Wani magidanci mai suna David Jafaru mai shekaru 35 yana zaune ne a Kaduna, yana sana’ar tuka babur ne a lokacin da ya yi hatsari ya karya kafarsa. Hakan ya tilasta masa komawa gida a garin Dogon Noma don jinya.
Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMuryoyin Shiri: Akila Jibrin
Fassara: Rukayya SaeedEdita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
Maryam Adam, mace mai tsananin rashin son kai ta dauki matsayin uwa da uba tun tana karama.
An tilasta mata zama uwa tana da shekaru 13, an tilasta mata barin makaranta, ta gudu daga tashin hankali, kuma ta koma gudun hijira. Da duk abin da ta shiga, ta kuduri aniyar baiwa 'ya'yanta rayuwa mai inganci.
Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMuryoyin Shiri: Khadija Gidado
Fassara: Rukayya SaeedEdita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
Kwanaki 105 Bilyaminu yana hannun masu garkuwa da mutane. A lokacin, iyalinsa sun yi duk abin da za su iya don tara kudin fansa da suka nema, ciki har da sanya gidajensu da gonakinsu don sayarwa. Amma hakan ya kasance da wahala sosai saboda manufar sake fasalin Naira ta Najeriya a wancan lokacin.
Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMuryoyin Shiri: Akila Jibrin
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
Wannan shiri na #BirbishinRikici ya koma ne a lokacin da Najeriya ke fama da matsalar kudi inda a wani yunkuri na dakile tallafin ayyukan ta'addanci, babban bankin Najeriya ya bullo da sabbin tsare-tsare. Muna nazarin nasarorin manufofin yayin da wadanda suka tsira kamar Maimuna suka kwashe kwanaki a tsare har sai an biya kudin fansa.
Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMuryoyin Shiri: Khadija Gidado
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
Salamatu Buhari, mai shekaru 20, tana aiki a gonarta, tana da juna biyu, a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka mamaye kauyensu. Sai suka fara kashe mazaje suna yiwa mata fyade, ta ji sai ta ruga don ta kare kanta. A tsakiyar daji ta shiga naƙuda.
Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuciya: Zubaida Baba Ibrahim
Muryoyin Shiri: Khadija Gidado
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
An sace Lilian Daniel, ‘yar shekara 20 daliba a Jami’ar Maiduguri a shekarar 2020 a lokacin da take komawa makaranta daga Jos a arewa ta tsakiyar Najeriya. Har yau babu wata magana kai tsaye daga gare ta. Wasiƙar baƙin ciki ɗaya kaɗai daga bauta.
Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuciya: Hauwa Shaffi Nuhu
Muryoyin Shiri: Khadija Gidado
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
A ranar 25 ga Fabrairu shekarar 2014, 'yan ta'addar Boko Haram sun kai hari a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Buni Yadi a Arewa maso Gabashin Najeriya. Sun kashe akalla ’yan makaranta matasa 29 a lokacin da suke kwana a dakunan kwanansu tare da kona dukkan gine-gine tun daga dakunan kwanan dalibai har zuwa ajujuwa. Sai masallacin ya tsira. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Marubuciya: Hauwa Shaffi Nuhu
Muryoyin Shiri: Khadija Gidado
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
Labarin Jummai da aka yi garkuwa da ita ya nuna wa daruruwan wasu mata da ake sacewa daga gidajensu, dakunan kwanan su, filayen gonaki, ko kuma lokacin da suke tafiya a yankuna da dama na arewa maso gabas. Saurari labarin juriya da jarumtaka da tayi akan wadanda sukayi garkuwa da ita.
Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuci: Ahmad Salkida
Muryoyin Shiri: Khadija GidadoFassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
Ahmadu Aga ya tuna rayuwarsa a baya a garin Boboshe, al’ummar da ke tsakiyar Borno da shauki.
Yana daya daga cikin sama da mutane miliyan biyu da aka tilastawa barin garuruwansu zuwa wuraren da suka fi tsaro a Najeriya da kasashen makwabta na Chadi, Nijar da Kamaru.
Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuci: Murtala Abdullahi
Muryoyin Shiri: Akila JibrinFassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
Aminu manomi ne a Daki Takwas, wani gari da ke Arewacin Najeriya. Amma ya kasa zuwa gonarsa saboda yawaitar sace mutane da ake da yaki karewa. Don haka rayuwa ta yi masa tsauri.
Mun bibibiyi labarin Aminu, wanda dalibi ne da ya dogara da aikin gona don biyan kudin makaranta. Anma wuyar aikin a yanzu saboda tashin hankali ta janyo masa abin da ba zai manta ba.
Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Marubuciya: Aisha Tijjani Jidda
Muryoyin Shiri: Sameer SherrifFassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
Wataƙila mutanen da suka rasa matsugunansu sun riga sun yi asara mai yawa saboda tashe-tashen hankula a arewa maso gabashin Najeriya, ‘yan uwansu, gidajensu, rayuwarsu, hankalinsu… Ta hanyar abubuwan da Hauwa, 14, da Adama, 22, za mu ga yadda yake da wuya a sami adalci ga wadanda aka yi wa fyade da kuma yadda rayuwarsu ta canza ba tare da jin dadi ba bayan cin zarafi.
Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuciya: Aisha Tijjani Jidda
Muryoyin Shiri: Khadija Gidado, Sabiqah Abdul-Ghaniy, Hauwa Abubakar SalehFassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media
-
Kusan shekaru goma ke nan da Hauwa ta bar garinsu na Gwoza, har zuwa yau ta kasance ‘yar gudun hijirar da ke fuskantar kuncin rayuwa da ba za ta iya jurewa ba a babban birnin tarayyar Najeriya.
Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Marubuciya: Rukayya Saeed
Muryoyin Shiri: Khadija Gidado
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media - Mostrar mais