Episodios
-
Ko kun san cewa har yanzu ana gudanar da al-adar nan ta sayen baki a Kasar Hausa idan an yi aure? Shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya yi nazari a kai.
-
Tsarin karatun Allo na neman ilimin da gwamnatin jihar Borno a Najeriya ke kokarin kyautatawa
-
¿Faltan episodios?
-
Shirin na al'adu ya duba tasirin gidan tarihi na Arewa (Arewa House) da ke Kaduna da ya tattara tarihin Marigayi Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da al'adu da sana'o'in yankin Arewacin Najeriya.
-
Shirin ya duba al'adar kacici-kacici ko wasa kwakwalwa da malam Bahaushe ke amfani da ita wajen ilimantawa.
-
Shirin ya mayar da hankali ne kan masarautar Wurkun da ke karamar hukumar Karim Lamido a Jihar Taraba da ke tarayyar Najeriya,
-
Shirin ya duba al'adar Masquerade, ko Basaje kamar yadda ake fassarawa, da ta kafu a yankin Kabilar Igbo a Najeriya.
-
Shirin ya duba fadi tashin da kungiyar Fudeco ke yi don ceto al'adun Fulani tare tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu da sauran al'umma
-
Shirin ya duba takaddamar da ta barke a bikin cika shekaru 75 da fara bikin bajekolin litattafai na birnin Frankfurt na Jamus.
-
Al'adar shan barasa na shekara-shekara a birnin Munich na Jamus
-
Shadi, dadaddiyar al'ada ce ta Fulani da aka fi amfani da ita wajen neman aure. Sai dai a yanzu al'amura sun sauya. Ko ya al'adar ta shadi take gudana a yanzu? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Shirin ya duba yadda wakokin baka ke kasance kamar wani tubali na gina al’umma, wanda ta hanyarsa ne ake samun ilimi, tarbiyya da kuma bunkasar tattalin arziki.
-
Shigowar zamani na neman kawar da maroka da sankira
-
Guda: Wata al'ada ce da ake yi ga sarakuna da kuma amare da angwaye yayin bukukuwa a Kasar Hausa. Ko kun san tasirin guda ga angwaye da ma amare? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Sha'irai mawakan Manzon Allah da Ahlil baitin gidansa da kuma waliyyai na karuwa a tsakanin matasa a Jamhuriyar Nijar.
-
Shirin ya duba yadda 'yan Afirka ke gudanaar da addinansu da ibadansu a kasar Jamus inda suke da zama. Wai shin suna zuwa masallantai da majami'u?
-
Ko kun san cewa akwai wasu tarin kabilu a jihar Kaduna da ke Tarayyar Najeriya, wadanda suka alkinta wasanni da al'adunsu? Shirin Taba Ka Lashe ya tattauna da su.
-
Shirin ya duba busa algaita da ake yi a lokacin taron sarakuna ko biki ko wata haduwa a tsakanin Barebari ko Kanuri.
-
Wani wuri a Zuru da ke jahar Kebbi ana kiransa da suna (Girmace), a wannan wuri ne da mutane ke rayuwa tare da Kadoji.
-
Masarautun gargajiya na zama tushen shugabanci da jagorancin al'ummar arewacin Najeriya, wanda ko a zamanin Turawan mulkin mallaka an ga yadda suka tafi tare da su. Sarakuna kan zamo alkiblar al'umma ta fuskar gudanar da rayuwa da dukkan al'amura na yau da kullum, kama daga harkokin neman ilimi da kasuwanci da zamantakewa da sana'o'i da dukkan lamuran da suka shafi al'adu da ma addinai.
-
Akwai lokacin da 'yan bori da matsafa ke haduwa a sassan yammacin Jamhuriyar Nijar.
- Mostrar más