Episodi
-
Bayan dunbum falala, da yawan samuwar ibadun dake kara kusanta bayi ga ubangijin su, da azumin watan ramadana ke zuwa dashi kamar yadda malamai suka saba fada mana, Hakazalika Kuma a watan na Ramadan dai na zuwa da wata alada mai dimbin tarihi dake debe wa alumma musamman na arewacin Najeriya kewa.
Wannan aladar itace ta tashe da ake fara yinta da Zarar watan azumi ya kai kwanaki goma.
Maza da mata na gudanar da wannan alada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da bat da kama, su ringa zagayawa gidaje da kwararo kwararo dauke da ganga da kayan kade kade suna bugawa suna waka.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan wannan dadaddiyar aladar, don jin inda ta samo asali, tarihin ta, da kuma yadda ake Gudanar da ita. -
Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana â wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta.
Sai dai wasu watan kan zo musu da kalubale â ba don sun shirya mishi b aba kuma don sun gaza shiryawa.
Wani rukunin wadannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan rayuwar mata zawarawa musamman a watan Ramadana. -
Episodi mancanti?
-
A duk lokacin da aka Éaura aure, wata adduâa da âyan uwa da abokan arziki kan yi ita ce âAllah Ya kawo Æazantar Éakiâ.
A alâadance, Éaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa.
Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waÉannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su. -
Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karbar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade.
Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma alâumma?
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da âyan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita. -
Zanen fuska na da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya musamman a kasar Hausa.
Sai dai wannan dadaddiyar alâada tana kan hanyar gushewa domin kuwa ba kasafai ake samun wadanda suke yin ta a wannan zamani ba.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan wannan alâada da kuma dalilin gushewar ta. -
A da akan kwashe kwanaki ana bukuwan aure a kasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin bik da zaman ajo zuwa budar kai da sayen baki.
Sai dai wadannan alâadu sannu a hankali suna ta gushewa.
Ko mene ne dalilin wannan sauyin?
Wannan ne batun da shirin Daga Laraba zai duba a wannan makon. -
Son haihuwar âyaâya maza fiye da âyaâya mata abu ne da ake samu tun tale-tale a tsakanin alummomi daban-daban.
A tsakanin wasu alâummomin, samun da namiji abin alfahari ne wanda kuma yake nuni da cigaba da dorewar ahali; sai dai ba a cika bai wa haihuwar âya mace irin wannan muhimmancin ba.
Ko wadanne dalilai ne suka sa wasu mutane suka fi son samun âyaâya maza a kan âyaâya mata?
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne a kan dalilan da suka sa mutane suka fi son haihuwar âyaâya maza a kan âyaâya mata. -
Samun ingattattun malamai a makarantun firamare da sakandare na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tubalin ingantaccen kuma nagartaccen ilimi a cikin alâumma.
Æorewar wannan fafutuka ta samar da ingantaccen ilimi kuma ta dogara ne a kan samun haziÆan matasa da za su maye gurbin malaman da ake da su yanzu.
Sai dai a Najeriya, alamu suna nuni da yadda matasa da dama suke gudun aikin koyarwa, musamman a kananan makarantu.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari a kan dalilan da suka sa haka. -
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san alâadar nan ta bayar da ko karÉo Éa ko 'ya riÆo.
A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don Æashin kansu.
Wannan alada ana yin ta ne da zimmar yauÆaÆa danÆon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuÉin sabulu.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan matsalar âyaâya da iyayen riko. -
A tsakanin Hausawa, sunaye masu alaka da harshen Larabci sun kusan maye gurbin na gargajiya irin su Tanko da Talle da Audi da dai sauran su.
Sai dai yayin da a da sunayen da Hausawa kan sanya wa âyaâyansu na Annabawa ko Sahabbai ko mashahuran malaman Muslunci ne, a baya-bayan nan wasu iyaye kan aro wasu kalmomi su rika kiran âyaâyansu da su.
Mene ne dalilin hakan, yaushe kuma daga ina ya samo asali, kuma mene ne tasirinsa a alâadance da ma a addinance?
Amsoshin wadannan da ma wasu tambayoyi makamantansu shirin Daga Laraba na wannan makon zai binciko
-
A da soyayya na kafuwa ne sakamakon gaskiyar mutum, ko nasabarsa, ko tarbiyyarsa ko kuma riko da addininsa.
Mace kan so saurayinta ko da kuwa ba shi da ko anini, a wasu lokutan ma ko da wani mai hannu da shuni ya fito takan tubure ta ki shi.
Sai dai a wannan zamani mata da dama kan fito fili suna bayyana irin saurayin da suke so, a galibin lokuta mai abin hannu.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan matan wannan zamanin na kin auren talaka.
-
A dukkan kwanakin karshen watan Disambar kowace shekara, lokacin ne da farin ciki ke cika a fuskokin Mabiya Yesu Almasihu don gudanar da bukuwaN ranar tunawa da haihuwar sa wato kirsimeti.
Sai dai, wasu darikun addinin kirista da suka hada seventh day Adventist, Jehovah Witness da ma kuma darikar Deeper Life basu yadda da gudanar da wannan biki na kirsimeti ba.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi Nazari ne kan wannan batu don gano dalilan da suka sa wadannan dariku basa bikin kirsimeti. -
Tururuwar da mutane suke yi zuwa manyan biranen Najeriya na barazana ga wadannan alÆaryu ta fuskar tsaftar muhalli.
Misali, wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa a duk sa'a daya birnin Legas kan yi baÆi 77 â hakan kuma kan haddasa karuwar sharar da ake zubarwa.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan yadda shara ke addabar wasu manyan biranen Najeriya da tasirinta a kan lafiyar jiki da ta muhalli. -
A karshe dai an ayyana John Mahama a matsayin zababben shugaban kasar Ghana bayan da alâummar kasar sun yanke shawarar zabensa lokacin da suka kada kuriâa ranar Asabar din da ta gabata.
Duk da sauran âyan Takara da John Mahama ya kara da su, ciki harda mataimakin shugaban kasar mai ci a yanzu wato Mahamudu Bawumia Musulmi na farko da ya tsaya takarar shugabancin kasar.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zaiyi Nazari ne kan nasarar da John Mahama ya samu a zaben kasar Ghna da kuma kalubalen da zai iya fuskanta a shekara daya na farkon waâadin sa. -
Kishin kasa na cikin abubuwan da shugabanni, da sauran masu ruwa da tsaki suke kira ga âyan Najeriya a kullum a kansu.
Muhimmancin kishin kasa ga cigaban alâumma, musamman a kasa mai kabilu da addinai daban-daban irin Najeriya, abu ne da ba zai misaltu ba.
Sai dai alamu na nuna cewa yan Najeriya sun fi nuna kishin kabilun da suka fito idan aka kwatanta da kishin kasar da suke da shi.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan wannan batu. -
Matsalar tsaro na daga cikin batutuwan da suka hana kasar nan cikas a âyan shekarun nan.
Kuma kamar yadda alumma ke bayyanawa akwai karancin jamiâan tsaro da ya kamata ace suna lura, tare da kiyaye rayuka da dukiyoyin alumma a koda yaushe.
Karancin jamiâan tsaron ne ya sa wasu daga cikin jihohin da rashin tsaron yafi kamari suka samar da wasu jamiâan tsaro dake taimaka wa jamiâan tsaron gwamnati wajen dakile haren haren da yan taâadda ke kaiwa a wasu yankunan kasar nan.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zaiyi duba ne kan wannan batu. -
An daÉe ana muhawara, musamman a Arewacin Najeriya, a kan buÆatar yin garambawul ga tsarin makarantun tsangaya.
A baya dai waÉannan makarantu kan samar da mahaddata alqurâani waÉanda kuma sukan dogara da kai
Sai dai a wannan zamani, yaran da suke karatu a ÆarÆashin tsarin sun zama mabarata.
Gwamnatoci da dama dai sun yi kokarin yin garambawul ga yadda ake gudanar da tsarin, amma ga alama haÆa ta kasa cimma ruwa.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi Nazari ne kan hanyoyin da za a bi don magance matsalolin da suka dabaibaye harkar. -
A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara â hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar âalmajiriâ idan ana nufin mabaraci.
Amma a da ba haka lamarin yake ba â almajiri bay a bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan zamani da ma irin halin da almajirai suka tsinci kan su a ciki. -
Kalmar almajiri ta samo asali ne daga yaren larabci wato almuhajir, dake nufin wanda ya bar garin sa don zuwa wani gari neman ilimi.
Mafi yawan alummar arewa inda akafi sanin Kalmar sun taso ne sun ga ana gudanar da karatun allo ko almajirci, wanda hakan ke nufin almajirci ya samo asali ne tun lokacin da musulunci ya fara shigowa Najeriya daga garin Maidugurin Jihar Borno zuwa kasar Hausa.
Shirin Daga Larab na wannan mako yayi duba ne kan tarihin almajirci da kuma yadda yake a da can baya. -
Taron da Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta yi a Kaduna ya bar baya da kuriaâa.
Daya daga cikin shawarwarin da gwamnonin suka yanke ita ce ta kin amincewa da wani Kuduri da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai Majalisar Dokoki ta Kasa.
Shin kishin Arewa ne ya sa gwamnonin suka yi Allah-wadai da Kudurin ko kuma son zuciya?
Wannan ce muhawarar da ta biyo bayan sanarwar bayan taron na NGF, kuma shirin Daga Laraba zai lalubo amsarta. - Mostra di più